GYARA KAYANKA
Salam a yau insha Allah gyaran mu shine abinda ake bukatar aunawa idan zaa dinka riga peplum.
To guraren da ake bukatar aunawa idan zaa dinka riga peplum sune kamar haka -
Kafada
Shoulder to burst - wato daga kafada zuwa nipple.
Shoulder to under burst - wato daga kafada zuwa kasan burst.
Half length - daga kafada zuwa inda flare din rigar zai fara.
Tsayin rigar - wato daga kafada zuwa inda mace yakeso ya tsaya wasu na tsayawa dai dai hips din mace wasu na so ya wuce hips.
Burs - wato zagayen kirji.
Under burst - wato zagayen kasan kirji.
Waist - zagayen kugu
Tsayin hannun rigar
Fadin hannun rigar
Fadin daga nipple din hagu zuwa nipple din dama
Wannan sune abinda kuke bukatar aunawa domin dinka riga peplum wato mai flare kenan.
Zamu fada muku na gown nan gaba insha Allah.
0 Comments