wanda bata kalla ba sai taje hausa fashion tv a youtube zataga yanda ake yanka riga peplum part1 shine videon
amma dukda haka zan dan kara yin bayani kadan akan yanda ake yankan
da farko idan kika dakko yadinki zaki shimfida shi a kan table kamar haka yanda zaku gani a hoto sai ki ninka yadin biyu ya yanda bayan kin ninka yadin zai zama inci 18, (wannan ba standard bane bane) saboda tanada kiba ne me wannan rigan shiyasa na auna inci 18 i dan kuma a atamfan ne zaki yanka yadi daya zaki cire kawai ki yanka saman rigan dashi.
To bayani na ninke inci 18 sai na zana layin kafada a ta saman sannan daga Layin kafadan sai na auna da tape dina ya taho kasa har zuwa inci 16 1/2 wannan tsayin half cut din rigan.
Half cut din rigan 15 ne na auna 16 1/2 ne saboda idan na hada tsakiyar rigan da gefen, zai dan zoba kadan to kinga idan na yanke inda ya zoba to tsayin half cut din zai rage sannan kuma aciki na hada da incin da zai fita na dinkin sama dana kasa shiyasa na auna inci 16 1/2.
Sannan daga shoulder line zuwa inda shape din breast cup zai fara shine nasa 8, sannan daga layin shoulder zuwa asalin inda tsakiyar breast cup shine nasa 11, that is shoulder to bust saboda shoulder to bust dinta 10 1/2/ne kinga dukda rabin inci 1/2 da zai fita na dinkin sama shine na auna 11.
sannan a layin shoulder na auna inci 7, a layin breast cup na auna inci 4 1/2, a layin kasan na auna inci 4 daga nan sai nayi amfani da chalk na zama shepe din tsakiyar gaban rigan kamar haka.
Daga nan sai na auna inci 2 a layin kasan half cut bayan tsakiyar rigan kenan sannan nayi amfani da chalk naja layi ya yafi sama har zuwa inda shape din breast din mu zai tsaya ta kasa kenan.
Sannan a ta saman rigan ta gurin layin kafadan na auna inci 1 1/2
daga nan sai nayi amfani da chalk na fitar dashape din breast cup din kamar yanda zaki gani a hoto
Bayan nan sai nayi amfani da almakashi na yanka shape din da zana da chalk da na gefen wato shape din gurin breast cup,
Bayan na yanka ne sai na dauki tsakiyar gaban na dai daita shi kamar yanda zaki gani a hoto
To yanxu ne zamu fara auna measurement din bust da waist ko ince measurement din under bust .
A layin shoulder na auna inci 8 saboda fadin kafadan ta 16 ne kinga 8+8=16 tinda ai ninki biyu ne
sannan sai na kara inci 1 1/2 na dinkin gurin hannu da kuma dinkin tsakiyar rigan da gefen
Tsayin gurin hannu na auna 8 1/2 sai nayi shaida da chalk sannan na zana layi kamar yanda zaki gani a hoto
To daga nan sai na auna bust din rigan, bust dinta 46 ne to 46÷4=11 1/2 to sai na auna 11 1/2/na kuma kara inci 2 1/2 allowance kenan
Sannan nayi amfani da chalk na zana shape din armhole wato ramin hannu kenan
Daga nan sai na auna measurement din under bust din rigan, under bust dinta 40 ne, Kunga 40÷4=10 to sai na auna 10 sannan na kara inci 3 na allowance, daga nan sai nayi amfani da chalk na zana shape din kamar yanda zaku gani a hoto sannan nayi amfani da almakashi na yanka.
Shikenan mun gama da yanka gaban rigan yanxu abinda ya rage shine yankan bayan
To abinda kawai zamuyi shine mu dauki gaban mu shimfida akan sauran yadin sannan mu bar inci daya da quarter ko da Rani allowance din saka zip a bayan rigar kenan daga nan sai muyi shape din gaban mu cofe mu yanka bayan.
Bayan muyi copying din gaban mun yanka bayan sai muzo mu yanka gurin shape din breast cup a tsakiyar bayan rigan
Shikenan yanxu mun gama da yankan saman doguwar rigar mu saura kasan kenan
yanzu zamu yanka kasan rigar
da farko zaki cire incin tsayin half cut din rigan saiki kirga kiganin inci nawa ya rge yacikashe full length din rigan to abinda ya rage yacikashe stayin rigan shine stawon flare din mu.
to sai kiauna tsayin flare din sai ki kara inci 2 na dinkin saman dana kalmasan kasan rigan
bayan kin yanka zaki ninka shi tsayin flare din yazama biyu ma'ana barin gaba dana baya kenan daganan sai ki shimfida akn table a bangaren bayan saiki bar inci daya da rabi allouwanc din gurin zip kenan kamar haka.
daganan saiki daidata saman rigan ki auna gabadaya abinda awon fadin kasan half cut din ya baki to shine fadin saman flare din kamar haka
bayanki auna to kawai abinda zakiyi shine kisa ruler dag gurin da kika auna fadn saman flare din sa kwai kifara bude shi daga nan har zuwa kasan rigan kamar haka
bayan nan saiki auna inci daga kasan flre din kama yanda kike gni a hoto daga nan sai kisa almakashi ki yanka.
1 Comments
Muna godiya
ReplyDelete