KAYAN AIKI GUDA GOMA DA AKE BUKATA DOMIN FARA KOYAN DINKI
Kayan aiki sune abu na farko da mutum zai fara tanza a yayin da ya yanke cewa yanso ya koyi dinki saboda bayan daza'ayi mutum yazama yana koyon wani aiki amma baya kwatanta yin aikin bayan ya koya yanda akeyi.
inkuma kunason akwatin daya tattara dukka wa'innan kayan aikin zaku iya siya online cikin farashi me sauki kuma za,a kawo muku shi ha kofar gidanku,ku danna wannan link dinhttps://amzn.to/2wt54Yd
Shiyasa ayau zamu fada muku kayan aiki guda 10 Wanda zaku tanaza ku fara dasu, akwai kayan aikin dinki dayawa Amma Kuna iya farawa da wa inda suka zama dole.
1 KEKEN DINKI : keken dinki shine Abu na farko kuma me muhimmaci da duk wani me sha'awar
fara koyon dinki zai tanaza domin yin gwajin abinda ka koya akoda yaushe. Saboda haka mutum yakamata ya nemi keken dinki me kyau ya siya electric ko manual ko sabo ko na hannu me kyau dai Wanda baxa ta wahalar da mutum ba saboda tsufan ta ko wani matsala.
2 ALMAKASHI : Abu na biyu shine almakashi me kaifi babba ko karami wanda dai kafi iya amfani
dashi na karfe ne ko na roba yazama dai yana da kaifi yanda zai fitar da yanka dai dai yanda ake bukata.
3 MEASURING TAPE : igiyar awon shine abu mafi muhimmanci a gurin tela wanda yakamata mutum ya tanaza domin fara koyon sana'ar dinki bayan keken dinki da almakashi, saboda dashi ne zaka ringaamfani gturin awon yadi sannan kuma kayi awon masu kawo dinki, duk da tape akeyi.
4 DUTSEN GUGA : dutsen ma abune mai matukar amfani a dinki dukda wasu naganin za'a iya yin wasu dinkuna batare da dutsen guga ba amma ni agani na idan anaso dinki yayi kyau to dutsen guga dolene.
5 TEBURIN YANKA : idan da hali mutum yakamata ya mallaki teburin yanka me kyau yazama
very smooth Wanda yadi zai kwanta lif akai batare da tangarda ba idan ba hali mutum na iya farawa dayin yankan yadin sa a kasa duk muma da haka muka fara.
6 ALLURAN KEKE : yakamata ace mutum ya tanaji extra sewing niddles wato alluran keke
saboda kar sai mutum na cikin aiki kawai sai allura ta karye ya tashi ya tafi neman allura. Idan kariga ka tanaje extra to bakada bukatan ka tashi sai dai ka sake wata alluran kawai ka cigaba.
7 EXTRA BOBBINS : bobbin sune hausawa ke kira da dan tariya ko wasu suce rila shima yana da kyau me dinki ya mallakesu da yawa koda irin guda biyar 5 ko fiye da haka.
8 LITTAFIN RUBUTU DA PENCIL KO BIRO : dole a tanaza littafin rubutu da biro don rubuta measurement da sketching.
9 ALLURAN HANNU : a zamanin da idan mutum zai fara koyon dinki ba'a barin sa yafara hawa keken dinki sai yafara da yin dinki da alluran hannu amma yanzu zamani ya canza duk wannan wahalar wa ne kawai abar mutum yatafi straight ya fara hawa keke shi yafi, amma dukda haka kuna bukatan allura don saka botir flower da sauransu.
10 RULER : agurin wasu ruler ba dole bane amma gameson pattern din sa yafita yanda yakamat to sai yayi amfani daruler
Domin samun hotunan styles masu kya fiye da 200 sai ku Danna nan domin downloading din sabon Android phone din mu Endless Ankara Styles
1 Comments
Allah ya bada lada
ReplyDelete