Tufafi basuda wani amfani sai yayin da wani dan adam yasaka su ajikinsa.
ma'ana wando ko riga amfaninsu bai cika sai yayin da mutum ya daurasu ajikinsa,
haka kuma kamar yanda masu iya magana suke cewa sutura cikar mutum ma'ana duk duk girman mutum sai yasaka sutura sannan sannan matsayinsa yake cika
shiyasa a yau zamu kawo muku hotunana tsararrun dogayen riguna da ake yayi masu daukar ido har guda 20,
wainnankayan sun kasance masu daukar idone saboda duk wani dinki da aka dinka sannan akayi masa ado da wani kallan yadi daban wanda ya dace to zakuga wannan dinkin na daukar idon jama'a sosai.
zamuyi muku bayanin wasu daga cikin hotunan da zamu zubo muku ( wato yanda akayi su, kallan yadin, kallan wuyan rigan, hannun rigan dakuma irin sha'anin da yafi dacewa a saka su).
DOGUWAR RIGA BAKA MAI TASWIRAR (A)
wannan doguwar rigar anyi ta ne da bakin yadi plain ma'ana wanda bazane ajikin sa, sai akayi wa rigar ado da pattern masu kyau wanda akaciresu daga jikin atamfa, shape din pattern din zakugansu kamar circle pattern din sunada kaloli guda biyu zakuga wasu yellow wasu kuma orange anyi rigar ne me shape din A.
wuyan rigar round neck ne da dan wanitsagu a ta tsakiyan wuyan, hannun rigan dogon hannu ne rabin hannun flare ne wato ya bude sosaiwanda anyi flare din ne da atamfar da aka ire pattern din da akayi ado dasu a gaban rigar
anyi ado da patterns din atamfarne ata kasan rigan daga irin gurin waist din rigan har zuwa kasa inda aka garwaya yello pattern da kuma orange aka jerasu yanda suka fitar da rigar tayi kyau sosai ana sakawa aje biki walima party da sauransu.
wow kai anyi amfani da hikima sosai wannan rigar, wannan doguwar riga dai an dinka ta ne leshi blue me shara shara wanda akayi mata shafi wato lining da bridal citin kalan leshin, wuyan rigar round neck ne hannun rigar 3 quater ne wato ya dan wuce gwuiwar hannu anyiwa rigar kwalliya da yadin atamfa me kala kala ajikinsa har kusan kala hudu ajikin sa amma flower dake jikin atamfar kanan flower ne anyanka atamfar ne dogayen kyallaye sannan aka ninka akayi ironing ta yanda za'a iya daurawa a dinka a saman leshin, anyi masa ado da dogayen layuka guda biyu a ta tsakiyar rigan sannan aka kara yin wasu layuka bibbiyu a ta gefen rigan wanda suka taho har zuwa kasan rigar bibbiyu bibbiyu sau biyar sannan kuma akabi kowani layi da kananan stones , ana iya saka wannan rigar agurin biki suna walima da dai sauran occassions.
2 Comments
Gaskiya sunyi kyau sosai
ReplyDeleteThis comment has been removed by the author.
ReplyDelete