Header Ads Widget

yanda ake yanka skirt six pieces



measurement din da zamuyi amfani dashi sune kamar haka:




tsayin skirt - 42

hips - 40

waist - 36

waist to knee - 18




sai mufara :-


dafarko idan ka dakko atamfar ka zakashimfida shi akan table ka ninka inci 9 kamar haka amma wannan inci 9 ba standard bane ma'ana zaka iya sawa yafi haka koma yazama br kai haka ba ya danganta yanda kakeso kasan skirt din ya bude.


https://hausadinki.blogspot.com/2020/07/yanda-ake-yanka-skirt-six-pieces.html?m=1


idan kumakanason kakalla video ne gashinan a kasa.



bayan ka ninkashi haka sai kayi amfani da ruler kazana traight

line a kwance, wannan shine layin gurin waist. daga wannan layin sai ka auna inci 9 yataho kasa sai kayi shaida da chalk ka zana layi a gurin da kayi shaida wannan layin shine hip line,

 (wato inda shape din hips din skirt din zai kasance)


 sannnan still daga waist line sai ka kara auna inci 18 ya taho kasa sai kayi shaida da chalk, shima ka sa ruler ka zana layi wannan shine layin gurin gwuiwa kenan wato our waist to knee kenan.


daga nan saika auna tsayin skirt din kakara inci daya da rabi 1 1/2 shima kayi shaida da chalk sannan ka zana layi a gurin.



to yanzu a layin waist ka auna inci 4, kayi shaida da chalk, a layin hips ka au nainci 4 1/2 kayi shaida da chalk, a layingwuiwa ka auna inci 4 kayi shaida da chalk, a layin kasan skirt din ka auna inci 9 kayi shaida da chalk.


daganan sai kayi amfani da ruler ka ringa hade layukan na gwuiwa ya hadu dana hip, na hip ya hadu dana waist na kasan skirt din ya hadu da na gwuiwa kamar haka,



sai kayi amfani da almakashi kabi patten din ka yanka.


wannan shine tsakiyar gaban skirt din


yanzu zamu fitar da tsakiyar bayan skirt din:-


to abinda zakayi bayan ka yanka na tsakiyar gaban kawai zaka kara ninka sauranyadin ta yanda zai zama inda yazama layin waist dinka a sauran yadin to yanzu shi zai koma layin kasan skirt kenan wato ka juyashi kasa ya koma sama kenan,


 sannan sai ka dauki stakiyar gaban ka shimfida shi akan sauran yadin, kabar zip allowance sanna ka zana shape din gurin sa zip din saboda ba straight ake barin gurin ba sai zana shape din  kamar haka sannan kayi amfanida almakashi kabi ka yanka  kamar haka.



yanzu kuma zamu yanka gefen skirt din :-


bayan ka stakiyar bayan skirt din sai ka kara ninka saura yadin ta yanda gurin da yazama saman skirt din a yayin yanka tsakiyar bayan skirt din yanzu zai koma shine kasan skirt din idan muka yanka gefen skirt din kenan wato zaka kara juyashi up side down.



bayan ka ninka shi sai ka aunainci 20 a gurin da zai zama kasan skirt din wannan ba standard banr zaka iya saka fiye da haka ko kuma abinda be kaiba wannan shineyake kara determining din budewar kasan skirt din idan kasa yafi 20 to kasan skirt din zai bude fiyeda idan kasa 20, yadai danganta da yanda kakeson shi.


taganan sai ka dauki stakiyar gaban ka daura akai kamar haka.





sai kabi shape din tsakiyar gaban ka yanka gefen skirt din kamar haka.



daga nan sai ka juya tsakiyar skirtdin ka daidai ta shi kamar haka



to yanzu ne zaka fara auna final measurement dinka da kuma final shape dinskirt din,

kamin nan yakamata ka kara da layukan da ka zana tin farko a jikin tsakiyar skirit din sune layin hips da layin gwuiwa kamar haka.





a layin hips ka auna measurement din hip /4 a measurement dina 40/4 zai bani 10 to zan auna 10 sain kara inci 2 1/2 na allowance sai inyi shaida da chalk, 


a layin waist ka auna measurement din waist/4 a measurement na  36/4 zai bani 9 to zan auna 9 sai inkara inci 1 kamin sai na kara inci 2 1/2 na allowance sai inyi shaida da chalk .


a layin gwuiwa kuwa zan auna duka abinda na samu ne a measurent din waist da allowance dinshi sai in zo in auna thesame abinda na samu a layin gwuiwar, daga nan sai nayi amfani da chalk na fitar da shape din skirt din kamar haka,



Sai kayiamfani da almakashi ka yanka



to yanxu na gama yanka six picies skirt amma zanyi copying din pecies din gefen tinda guda biyu na fitar to zaka kara ninka sauran yadin ta yanda zai isa ya fita da irin gefen sai ka shimfida gefen kabi shape dinsaka yanka.





Post a Comment

0 Comments