GYARA KAYANKA
Assalamu alaikum dafatan kuna lafiya ya gida ya ayyuka, alhamdulillah.
A yau in Allah ya yarda zamuyi magana akan meyasa idan kunyu yankan riga me breast curve sai ta ringa yin yawa ajikin mace bayan kuma kun yanka yanda muka nuna muku,
Wanna shine tambayan da wata tayi min, to abinda yake faruwa
yanda muka nuna muku bawai standard bane shiyasa muke fada
muku cewa na wannan da muka yanka awon ta ka zana amma ku
idan kunzo naku zaku sa abinda kuka auna ne.
Misali kamar gurin tazarar daga wannan breast din zuwa dayan
breast din ina yawan saka 4 da rabi a layin breast curve a laying
under burst kuma ina yawan saka 4 to sai wasu suka dauka wannan
standard ne aa ba standard bane idan wanda zaku dinkawa kayan
budurwa ce me tasowa yanxu zaku iya saka mata 4 a layin breast
curve sai 3 da rabi a layin under burst kunga tazarar breast to breast
zai zama inci bakwai kenan.
To amma abinda yafi shine ku ringa saka tape ajikin me kayan ku
auna nawa ne tazarar daga wannan breast din zuwa dayan.
Haka gurin curve din yawanci ina amfani da 6 ko 5 to shima
yakamata ku ringa aunawa daga saman breast din zuwa kasan din
abinda kuka samu to shine tsayin curve din Allah yasa kun fahimta
nagode.
1 Comments
Maa Shaa Allah
ReplyDelete