Header Ads Widget

YANDA AKE YANKA A SHAPE GOWN





Yankan free fited A line gown yafi kowani 
irin yanka sauki acikin dinki domin shi yankan A line gown ba ruwanshi da breast cut saima 
idan kaso zakasa zip


Abubuwan da zaku bukata gurin yankan sune kamar haka -

Measuring tape (igiyar awo)

Chalk (allin rubutu)

Almakashi

ruler (sandar zana layi)



To da  farko dai idan ka dakko atamfarka sai ka gwada tsawon rigar sai ka kara inch 2 biyu  sannan ka ninka abinda ka gwada daganan sai ka yanka, bayan ka yanka sai kakara raba abinda kayanka zuwa gida biyu wato (barin gaba dana baya kenan.




Daga nan sai ka shimfidasu akan table a ninke, Idan zakasa zip ne a bayan sai ka bar inchi daya  da rabi  1 ½ a bangaren bayan kamin ka fara yankawa


Daganan saika zana layin kafada, ka zana layin waist, ka zana layin armhole wato( gurin ramin hannu)  a wannan yankan zanyi amfani da measurement kamar haka


Shoulder 16

Bust 40

Waist 36


Yanzu zamu fara aunawa da fitar da taswirar yankan da zamuyi !

A layin kafadan saika gwada inchi 8 ½  sai kasa chalk kayi shaidan gurin daganan saika gwada daga kafada zuwa kasa inch 9 kasa chalk kayi shaida wannan shine gurin da zamu yanka ramin hannun mu wato armhole.



Daganan sai ka gwada inchi 4 ½ wannan shine fadin wiyan kenan sannan zurfin wuyan zamu saka inchi 7  Wannan wuyan gaban rigan ne idan kuma kanason gaba da bayan wuya su zama daya sai ka yanka su a tare, idan kuma kanason wuyan bayan yayi  sama ne saika zana sa yanda kakeso haka kuma idan kanaso yayi deep shima saika zana shi yanda kake so, a wannan inaso wuyan yayi sama ne, a layin bust sai ka gwada  40/4 = 10 sai ka gwada 10 ka kara inch daya saboda wannan free fited ne to zamu kara inchi 2 akan bust measurement dinmu sannan kuma zamu kara allowance a rigan na inchi 2 ko 3 saboda koda zuwa nan gaba idan me rigar ta kara k’iba za’a buda mata cikin sauki

sai kasa chalk  kayi shaidan gurin,

Haka shima gurin waist  line zaka gwada kayi calculating 36/4 = 9 saika gwada 9 ka kara inchi daya sannan ka kara inch 2 ½ na allowance daga nan sai kasa chalk kayi shaida


A ta kasan wato fadin kasan rigan kana iya gwada duk yanda kakeso idan me kayan naso kasan ya bude sai kabude shi idan kuma bataso ya bude saika gwada dan daidai sannan kasa chalk kayi shaida,  dagana sai ka dauki chalk dinka  kabi shaidodin dakayi ka zana shape din rigar.



Bayan ka gama zanawa sai kasa almakashinka kabi shape din da ka zana ka yanka.



Shikenan yanzu mungama da yankan riga abinda ya rage mana shine yankan hannun rigan wanda shin hannun rigan pencil hand zamu yanka.

Wato sai ka dakko sauran atamfar ka daidai ta shi ka ninka shi.


Daga nan sai ka gwada tsayin hannun ka kara inchi 1 ½ kayi shaida  da chalk ka zana sannan daga saman hannun ka gwada inchi 4 zuwa kasa idan bakason tattara a kafadan kenanan idan kuma kanason tattara sai  ka gwada inchi 8, a wannan banason tattara a kafadan so zan gwada inci hudu kenan.


Daga nan saika gwada daga saman hannun zuwa inci 10  ka zana layi  kayi shaida da chalk  to anan ne zaka gwada fadin hannun

sai ka kara inci biyu  2 na  allowance da dinki, a kasan hannun shima ka gwada yanda ka samu a measurement dinka shima ka kara inci biyu sai kasa chalk ka zana shape dinsa.



Sannan kasa almakashinka kabi zanen ka yanka sa kamar haka.




Alhamdulillah wanna shine yanda ake yanka A line gown wato (doguwar riga mai taswirar A) idan da tambaya kuna iya kuyi a comment nagode. 

ko ku kira yahya mohammed a 08147227378




Post a Comment

2 Comments

  1. Tambayata anan itace shin anasama ta atamfa lining ko ba a yimasa???

    ReplyDelete