off shoulder bouse kala kala ne sunkai gurin kala 4 koma sunfi hakan.
dinka off shoulder blouse ba bayani bane wanda za'a iya yi a facebook post kawai kuma ace mutum ya fahimta sosai yana bukata blog post ne da kuma isassun hotuna wanda zasu sa mutum ya gane ko kuma ayi video kawai hade da yin bayani amma yanda naga yan matan gidan nan da yawa naso su koyi yanda ake dinkawa shiyasa na ware lokaci zanyi muku bayanin yanda ake dinka kala daya a takaice in Allah yaso sauran sai muyi video ko kuma muyi rubutu a website din mu.
farko dai a wannan off shoulder da zamuyi shi ne a yankan shoulder breast cup ko kuma ince shoulder dat, na riga nayi video akan yanda ake yanka wa ga wanda bata kalla ba sai taje hausa fashion tv a youtube ta kalla.
measuremnt din da nayi amfani dashi sune-
shoulder 14.
bust 36.
waist(under bust) 30.
half cut 13.
shoulder to bust 10.
shoulder 14.
bust 36.
waist(under bust) 30.
half cut 13.
shoulder to bust 10.
to bayan kun yanka shoulder breast cup din ku kamar yanda muka koyar a baya sai ku yanka lining dinshi wato shafi kenan zaku gani acikin hotunan da muka dauka.
daga nan sai ku manna padded, bayan ku manna padded sai ku hade tsakiyan da gefen gaban sannan sai ku goge da iron shima akwai hoto,
bayan na hada na goge da dutsen guga ne , daga nan sai nayi shaping din rigan wato sai na fitar da shape din rigan.
bayan na hada na goge da dutsen guga ne , daga nan sai nayi shaping din rigan wato sai na fitar da shape din rigan.
kunsan yankan riga mai breast cup ba yanka bane wanda daga an yanka shikenan sai kawai acigaba da dinkawa har sai an gama a'a ba haka bane shi dinki idan kanaso yafita to dole yazama bayan kayi yanka to zaka ringa yin adjustment a gurin da ya dace ayi saboda kasamu measurement yanda yakamata.
saboda haka nayi shaping kamar yanda zaku ga hoton, shoulder 14 sai na kara rabin inci , tsaying gurin hannu nasaka 7 1/2 bust 36 sai nakara inci 2 1/2 allowance
sai waist ina nufin (under bust) measurement 30 shima na kara 2 1/2 allownce sannan nayi amfani da chalk na zana shape kamin na yanka shape din dana zana da almakashi kamar yanda zakunga hoton

yanzu zanyi amfani da hannun zaku ga shima yanda ake yanka shi,
sannan zakuma kuga yanda ake fitar da wuyan riga mai off shoulder irin wannan
Bayan kin yanka shape din wuyan da gurin hannun sai ki yanka lining din gaban rigan
karashen wuyan yana jikin hannun inda zakuga na gwad 3 1/2 inches daganan sai ku hadesu da lining din ku dinka sannan ku goge da da iron,

shima akwai hoto
sannan ku yanka bayan rigan wato idan baku riga kun yankasu baki daya ba gaba da bayan kenan zaku ga hoton sai ku yanka lining din ku dinka ku juwa sannan ku goge da dutsen guga.
daganan sa ku auna measurement din rigan ku zana shape din da chalk
bayan kunyi amfani da chalk kun zana shape din sai kuyi tracing din dayan gefen shima chalk din ya fito sannan sai ku hade gaban da bayan daga nan sai ku goge da dutsen guga kamar haka
daganan sai shima hannun ku hada shi, sai kun fara hade damtsen hannun kamin sai kuzo hadesu da rigan kamar yanda zaku gani a hoto
bayan kunyi amfani da chalk kun zana shape din sai kuyi tracing din dayan gefen shima chalk din ya fito sannan sai ku hade gaban da bayan daga nan sai ku goge da dutsen guga kamar haka
4 Comments
Mun gode kwarai Allah ya Saka da Alkhairi
ReplyDeleteGaskiya ba abinda xamuce se Allah ya saka d gidan Aljannah....wllh ba karamin karuwa muke ba
ReplyDeleteAlhamdulillah ameen ameen
DeleteMuna matukar godiya sosae Allah ya karo basira
ReplyDelete