da farko dai abubuwan da ake aunawa sun danganta da irin kalan dinkin da za'ayi saboda haka abin da zamuyi yanzu shine zamu koya muku yanda ake daukar awon yawancin abina ake bukata acikin kowani kalan dinkuna.
abinda zamuyi amfani dasu agurin daukar masurement guda 3 ne -
1 tape
2 littafin rubutu
3 biro ko pencil
lambobin dake jikin measuring tape kala biyune wato akwai centimtre sannan akwai inches to mafi saukin amfani shine inches saboda haka duk awon da zakayi kayi shi da inches ne.
mafi yawan guraren da ake aunawa sune -
1 fadin kafada
2 bust
3 under bust
4 tsayin riga
5 tsayin daga kafada zuwa breast point
6 tsayin half length
7 tsayin skirt
8 hip
9 waist
10 tsayin hannu
11 fadin hannu
12 daga kafada zuwa hips
kusan kowani kalan dinki ko ince mafi yawancin abinda ake aunawa indai dinkin mace ne basa wuce haka wato inda sikafi muhimmaci a awon dinki kenan!
1. fadin kafada ; fadin kafada ana auna shine daga farkon kafadan hagu zuwa farkon kafadan dama kamar haka.
2. bust ; Ana auna bust ne kamar haka wato zaka sa tape dinka ko tape dinki ki ya zagaye jikin ki ta gurin kirji har sai tape din ya dawo inda farkon sa ya fara.
3 under bust ; wannan shine zagayen kasan bust wato immediately daga inda breast cup ya kare nan ne ake kira under bust, zaka zura tape dinka ya zagayo daga bayan mace har sai yadawo inda farkon sa ya fara
4. tsayin riga ; zaki daura tape dinki ko tape dinka a kafadar mutum sai ka dafe shi da hannun hagu sannan kasa hannun daman ka ka janyo tape din har izuwa inda mai kaya takeson tsawon riganta ya tsaya ko dogon riga ne ko gajere.
5. tsayin daga kafada zuwa breast cup ; wannan shine shoulder to bust saboda wannan ya baban banta a jikin mace wata zaka ga shoulder to breast bust dinta 10 ne, wata 11, wata 12, wata 9 yadai danganta amma mafiya yawan mata yana zama 10 ne.
Domin samun hotunan styles masu kya fiye da 200 sai ku Danna nan domin downloading din sabon Android phone din mu Endless Ankara Styles
6. stayuin half lenght ; tsayin rabin riga wato misalin kamar idan rigan peplum ce wato me flare kennan to rabin saman shi a ke kira da half length, ana aunashi daga kafada zuwa inda akeso flare ya fara wasu nason flare yafara daga kasan breast cup, wasu kuma naso yafara daga waist duk dai yanda mace takeso sai ka auna.
7. stayin skirt ; ana auna tsayin skirt ne daga waist din mace har zuwa inda takeso tsayin skirt din ya tsaya wasu naso yayi tsawo har ya ringa rufe musu takalmi wasu kuma sunaso ya zama dai da tsawonsu ya danganta.
8. hip ; hip shine the widest part in the body after the waist, ana auna hips kamar haka zaki zura tape dinki ta baya har sai ya zagawo ya taba inda farkon tape din ki ya tsaya.
9. waist; shine kugu ana auna kugu ne yawnci idan za'a dink skirt, to shima dai zaki zura tape dinki ta baya har sai ya zagawo ya taba farkon tape din.
10. tsayin hannu ; ana aun tsayin hannu ne daga farkon kafada zuwa inda mutum keson tsayin hannun ya tsaya dogo ne, guntu ne, 3 quarter ko gajere duk yanda mutum keso.
Domin samun hotunan styles masu kyau ku danna wanna rubutunAnkara designers blog
11. fadin hannu ; ana auna fadin hannu mutum ne idan mace nason hannun ya kama koma dai koya mace takeson fadin sai ka auna kamar haka.
Domin samun hotunan styles masu kya fiye da 200 sai ku Danna nan domin downloading din sabon Android phone din mu Endless Ankara Styles
12. daga kafada zuwa hip; wannan shine the distance from shoulder to hip ana auna shine wayanci idan za'a dinka fitted gown saboda asan daga inane asalin hip din zai tsaya.
5 Comments
Allah ya kara basira muna gdy
ReplyDeleteMungode Allah ya saka da alkhairi
ReplyDeleteGskiya Alhamdulillah! Ina godiya da wannan bayanai dana samu a wannan shafin domin na amfana da abubwa dayawa a ciki, Allah ya biya,ameen
ReplyDeleteJazakhAllahu khair
ReplyDeleteMa shaa Allah Allah ya kara basira
ReplyDelete